Abu Ubaydah, kakakin rundunan Al-Qassam, ya sanar a cikin wata zazzafar sanarwa:
Mayakan na Mujahid dai na cikin shirin ko-ta-kwana kuma shirin mamaye birnin Gaza zai zama abin tsoro ga kwamandoji da shugabannin yahudawan sahyoniya. Sojojin Isra'ila za su biya farshin hakan da jinin sojojinsu, kuma yunkurin da Netanyahu da ministocinsa na 'yan Nazi za su yi zai samar da juriya da karin damammaki na kama fursunoni.
Za mu kare fursunonin abokan gaba gwargwadon iko. Za su kasance cikin yanayi iri daya da mayakan mu a yankunan da ake gwabzawa. Za mu sanar da mutuwar duk wani fursunan Isra'ila ta kashe a harin tare da sunansa, hotonsa da shaidar mutuwarsa.
Isra'ila Fara Kai Hare-Hare A Arewaci Da Gabashin Gaza
Da su ke bayyana Gaza a matsayin "yankin yaki mai hatsari," sojojin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a yankuna daban-daban na birnin, ciki har da al-Karama, al-Saftawi, da Abu Iskander, tare da kai hare-hare da bama-bamai a arewacin zirin Gaza. Mazauna yankin sun ce: "Isra’ila na ci gaba da lalata birnin Gaza a karkashin wutar bama-bamai".
A sa’i daya kuma Haɓakar ayyukan soji na mamaya ya gamu da babban martani na kasa da kasa; Turkiyya ta katse huldar tattalin arziki da sararin samaniyarta ga Isra'ila, kuma kasashen Turai da dama sun yi tir da harin da aka kai a Gaza. Sakatare Janar
Mummunan Tarko Ga Sojojin Isra’ila A Zaytuun | Dakarun Qassam Sun Kama Sojojin Isra'ila 4
Kafofin yada labaran yahudawan sun rawaito cewa, an gwabza kazamin fada tsakanin mayakan Qassam da sojojin Isra'ila a unguwar al-Zaytoun. A cewar wadannan majiyoyin, mayakan na Qassam da dama ne suka shiga wani kazamin harin kwantan bauna ga sojojin Isra'ila tare da kai hari kan sansanonin sojoji.
Jiragen sama masu saukar ungulu 6 na Isra'ila da aka aika domin kwashe sojoji suma sun fuskanci munanan bude wuta daga dakarun gwagwarmaya. Kafofin yada labarai na Ibraniyawa sun tabbatar da cewa sojoji hudu da suka bace a unguwar mai yiwuwa an kama su ne. Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun fara janye sojojinsu daga unguwar Zeytoun tare da mayar da su bariki.
Your Comment